Aikace-Aikacen Kemistiri -Application Of Chemistry

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Aikace-Aikacen Kemistiri (Application Of Chemistry)


Gabatarwa

Wannan rubutu ya ƙuduri aniyar lqa wasu fannonin kemistiri ya ga yadda suke amfani da kemistiri wajen samar da wasu abubuwa masu amfani a rayuwa. Ga ɗan abin da ya samu:

Kalli Wannan Bidiyon Domin Ƙarin Bayani

Fannin Kimiyyar Halittu (Biology)
A wannan fanni, kemistiri ya yi reshen da ake kira bayokesimitiri (Biochemistry) wanda ya mayar da hankali wajen nazartar cuɗanyar sinadarai (chemical reactions) da ke wakana a ciki da wajen halittu masu rai kamar abubuwan da suka shafi narkewar abinci (digestion); shiga da fitar numfashi (respiration and photosynthesis); nazarin tsarin sinadaran ƙwayoyin halittar jikin (chemical structure of cells) da sauran su.

Fannin Kmiyyar Fisiks (Physics)
Kemistiri yana gaurayuwa da fisiks a fannin da ake kira physical chemistry domin nazartar yanayi da kuma tsarin abubuwa haɗe da ɓangarorin da abubuwan suka ƙunsa (properties and structure of matter).

Fannin Likitanci da Harhaɗa Magunguna (Medicine and Pharmaceutical)
Magani, haɗe-haɗen sinadarai (chemicals) ne waɗanda ke warkar da cututtuka. Ana haɗa magani a ɗakunan gwaje-gwajen kimiyya (laboratories) ko kuma kai tsaye daga halittun Allah waɗanda ka iya zama tsirrai ko waninsu.

Kemistry yana bayar da gagarumar gudunmawa a waɗannan fannoni guda biyu; fannin lafiya da kuma harhaɗa magunguna ta hanyar sanin irin yanayi da kuma irin ayyukan da ƙwayoyin hallita kamar irin su enzymes da hormones ke yi a cikin jiki sannan ya yi bayanin irin gudunmawar da magani zai basu wajen kare lafiyar jiki da sauransu.

Fannin Gona (Agriculture)
A fannin aikin gona, kemistiri yana bayar da gudunmawowin da suka haɗa da:

  • Gano yanayin ƙasa da kuma irin shukar da za ta dace da ita.
  • Samar da sinadaran kashe ciyawa (herbicide).
  • Samar da sinadaran kashe ƙwari (pesticide).
  • Samar da sinadaran inganta amfanin gona kamar masu ƙarawa amfani ƙwarin jiki, samar da amfani (‘ya’ya) mai inganci.
  • Ƙara yawan haihuwar amfanin gona.
  • Sinadaran adana kayan amfanin gona, da sauransu.

Manazarta:


ACS Chemistry for Life (2020). Chemistry Careers. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.acs.org/content/acs/en/careers/college-to-career/chemistry-careers.html

AGCAS (2020). Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/careers-advice/what-can-i-do-with-my-degree/chemistry

AGCAS (2020). Nuclear engineer. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/job-profiles/nuclear-engineer

Better Health (2017). Workplace safety - hazardous substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.betterhealth.vic.gov.au/health/healthyliving/workplace-safety-hazardous-substances

Cleveland Clinic (2018). Household Chemical Products and Their Health Risk An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://my.cleɓelandclinic.org/health/articles/11397-household-chemical-products-and-their-health-risk

Mendeley (2018). Top Ten Chemistry Jobs. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.mendeley.com/careers/article/top-10-chemistry-jobs/

Moore J.T (2020). Ten Great Careers in Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.dummies.com/education/science/chemistry/ten-great-careers-in-chemistry

Tucker L. (2019). What Can You Do With a Chemistry Degree? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.topuniversities.com/student-info/careers-advice/what-can-you-do-chemistry-degree

United States Department of Labor (2020). Chemical Hazards and Toɗic Substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.osha.gov/SLTC/hazardoustoxicsubstances/


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub